• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Binciki Masu Daukar Bidiyon A. A. Rufa’I, Wani Lauya Ya Bukaci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

ByGlobal Tracker

Jul 24, 2023

Wani lauya Mai zaman a jihar Kano dake rajin kare hakkin Dan Adam Barista Badamasi Suleiman Gandu, rubuta takardar korafi ga Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano inda ya bukaci Rundunar Yan sandan Jihar ta binciki masu daukar Bidiyon wani A. A. Rufa’I wanda yake ikirarin yafi kowa kudi a duniya.

Takarar korafin ta kuma bukaci kare hakkin Mista Rufa’I da kuma lafiyar sa sakamakon yada Bidiyon na kara kawo tasgaro a kokarin da ake na kula da lafiyar sa.

Cikin kunshin takarar korafin wacce Barista Gandu ya sanyawa hanu dauke da kwanan watan 24 ga watan Yulin, 2023 wacce Kuma aka aikewa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf, lauyan ya roki gwamnatin jihar Kano ta ceto A. A. Rufa’I daga halin da yake ciki.

Takadar Mai taken “KORAFI KAN MASU DAUKAR BIDIYON A. A. RUFA’I” ta ce kamar yadda Allah ya Azurta Kano da Aliko Dangote da Abdussamadu Isyaka Rabi’u, haka ya Azurta ta da A. A. Rufa’I wanda yake ikirarin yafi kowa kudi a duniya sakamakon rashin lafiyar da yake fama da shi.

KU KARANTA: Rundunar Yan Sandan Kano ta Kama Matashin da ya Kashe Mahaifiyar sa.

A. A Rufa’I dai yayi ikirarin siyan Kano da Kaduna da Birnin Dubai a kasar Ingila da kasar Saudia da kuma wasu mayan kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Manchester United.

Barista Badamasi Suleiman Gandu dai ya ce ya rubuta takarar korafin ne dogaro da sashi na 12 (1) na dokar kare lafiyar Dan Adam na shekarar 2021 da kuma dokar kare lafiyar kowanne Dan kasa a sashi na 12 (2) (b).

Lauyan ya bukaci Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano da bada umarnin binciken masu dauka da kuma yada Bidiyon Mista Rufa’I domin kuma doka ta bada damar Alumma su Kai rahoton duk wanda yake daukar Bidiyon Kuma gaza yin hakan sabawa doka ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *