DAGA: Ibrahim Abubakar Diso, Kano
A kokarin ta na inganta harkokin ilimi da kuma koyo da koyarwa a yankin ta, majalisar Karamar hukumar Gwale da dauki Malaman makarantar firamare 20 Aiki.
Cikin wata sanarwa da Jami’ar yada labarai ta yankin ta aikowa GLOBAL TRACKER ta ambato shugaban Karamar hukumar Alhaji Kadalid Ishak Doso lokacin da yake Mika musu takardun daukar aikin na cewa hakan na daga cikin kokarin shugabancin yankin na rage matsalar karancin aikin yi.
Khalid Diso ya ce a ko da yaushe a shirye suke wajen tallafawa dai-daikun mutane ko Kungiyoyi domin cigaban fannin ilimin yankin.
Ya ce Allah ya albarkaci Karamar hukumar da damammaki kala-kala ta yadda al’ummar Gwale za su fara karatu tun daga Firamare har zuwa Jami’a duk a cikin yankin Karamar hukumar, la’akari da cewa Gwale ita ce Karamar hukumar da ta fi ko wacce yawan makarantun gaba da sikandire a fadin jihar Kano.
KU KARANTA: YANZU YANZU: Kawu Sumaila Ya Ci Zaben Sanatan Kano ta Kudu
Da suke bayyana godiya, wasu daga cikin wadanda aka dauka aikin Aisha Abubakar da Zakariyya Jafar sun Bada tabbacin jajircewa a aikin su kasancewar da ma a nan suka fi kwarewa.
A wani labarin kuma, shugaban Karamar hukumar Alhaji Kadalid Ishak Diso ya rantsar da masu bashi shawara su hudu da ya dauka domin taimaka masa a harkokin Siyasa.
Wanda aka dauka din sun Hadar da Zakariyya Jafar mataimaki na musamman a harkokin makarantun gaba da sikandire da Mubarak Muhammad mataimaki na musamman a harkokin karbar haraji da Nura Yusuf mataimaki na musamman a harkokin Hulda da sauran kananan Hukumomi sai kuma Yusuf Shehu mataimaki na musamman a harkokin ilimi.