• Mon. Sep 7th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Duk Matar Da Mijinta Ya Hanata Zabar APC, Ta Kashe Auren Ta Fito — Shugaban APC

BySani Magaji Garko

Sep 4, 2026

A dai-dai lokacin da aka fara tafiyar yada kanin wani a kamfen din yakin neman zaben 2027, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Yobe, Muhammad Gadaka, ya bukaci matan auren da mazajensu suka hanasu zabar APC a zaben 2027 su nemi saki, inda ya ce shi zai biya sadakinsu idan za su yi wani auren.

“Idan mijinki ya hanaki Zabar APC ki yi masa tawaye ki fito, Ni Zan Biya Sabon Sadakin,” inji Muhammad Gadaka.

Gadaka ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin yakin neman zabe a Nangere jiya Alhamis.

KU KARANTA: Kano Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Takalmin Taya Ta Farko a Nigeria 

A wani faifan bidiyo da aka wallafa, shugaban APC din ya ce matan da mazajensu ba za su bar su su zabi APC ba kawai su kashe auren.

Sai dai kalaman nasa sun jawo suka daga mazauna da malaman addinin Musulunci, wadanda suka bayyana su a matsayin masu tayar da hankali da kuma barazana ga darajar iyali.

Daga baya Gadaka ya nemi afuwa tare da janye kalaman nasa.

Ya bayyana cewa abin da ya fada wasa ne kawai, kuma ba ya wakiltar abin da ya yi imani da shi ko kuma yana nufin karfafa mutane su rabu da aurensu.

Kalaman shugaban APC na Yobe sun zo ne kwanaki kadan bayan kwamishinan matasa da wasanni na jihar Borno, Sainna Buba, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya yi barazanar yi wa mutanen da suka ki goyon bayan APC bulala a zaben 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *