• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

KANO: Mutane Uku Sun Mutu, An Kone Motar Yan sanda a Rigima Tsakanin Jami’an Tsaro Da Direban Babbar Mota a Wudil

BySani Magaji Garko

Jan 30, 2025

Akalla mutane Uku ne ciki harda Dan sanda guda daya ake zargin sun rasa rayuwakansu biyo bayan wani rikici da ya barke tsakanin jam’an yan sanda da al’umma a yankin kasuwar Darki dake karamar hukumar Wudil a jihar Kano.

Wani shaidar gani da ido ya gayawa GLOBAL TRACKER cewa hatsaniyar ta faro ne tsakanin wani direban babbar mota da jami’in yan sanda bayan da yaki bayar da na goro wato cin hanci ga jami’an inda suka dakatar da motarsa gami da yankar direban a fuska.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ne ya fusata fasinjojin motar suka fito tare da fara dukkan jami’in yan sandan, wanda hakan ne yasa suka harbi mutum biyu da rahotanni suka ce sun Mutu sai kuma jami’in Dan sanda da ya rasa ransa sakamakon dukan da fasinjoji suka yi masa.

KU KARANTA: Binciki Masu Daukar Bidiyon A. A. Rufa’I, Wani Lauya Ya Bukaci Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Tuni dai wasu rahotanni suka ce an kone motar yan sanda a gurin da lamarin ya faru.

“Yanzu dai kusan mutane Uku ne suka Mutu, mutane biyu yan sanda ne suka harbesu, sai kuma wani dan sanda da ake zargin shima ya mutu saboda dukan da fasinjojin motar suka yi masa,” inji wani Dan Kasuwa dake kasuwar ta Darki.

To sai dai GLOBAL TRACKER bata iya tantance adadin ba, Amma rahotanni since wanda aka fara harba kuma ya rasu ba’a wuce mako guda da auren sa ba.

Dama dai mutane sun sha kokawa da jami’an dake aiki a wannan waje inda suke fatan hukumomin da abin ya shafa zasu shiga cikin lamarin dan kawo dai-daito.

Wasu bayanai sun ce ko a makonnin da suka gabata sai da alummar yankin suka kaiwa babban baturen Yan sandan yankin korafin janye jami’an dake kafa shingen bincike duk ranar Alhamis (ranar Kasuwa) saboda yadda suke matsawa yan Kasuwa.

Idan za a iya tunawa dai ko a kwanaki baya sai da aka samu rasa rai bayan hatsaniya ta barke tsakanin jami’an tsaron sojoji dake yiwa mutane aski da wadanda suke zuwa kasuwar Darki inda har takai ga sun yiwa wani matashi dukan tsiya har takai ga ya rasa ransa.

Jaridar GLOBAL TRACKER ta tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa inda ya katse kiraye-kirayen da aka yi masa, kuma bai maido da sakon karta-kwana da aka aike masa ba.

Akwai Karin bayani….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *