Daga Rabiu Sanusi, Kano
Hukumar kidaya ta kasa reshen jihar Kano ano ta nesanta kanta da bayanan dake yawo na karbar naira 5,000 dan tabbatar da sunan Wandanda za suyi aikin wucin gadi na Kidaya.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Hajiya Jamila Abdulkadir ta fitar wacce ta rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce bisa bayanai da hukumar take samu daga jama’a ta sa jami’an tsaro su buncika lamarin.
Haka zalika sanarwa ta cigaba da cewa wadandan suke karbar kudin da sunan zasu tabbatar wa wanda ya cike gurbin aikin wucin gadi na kidaya basu da alaka da hukumar kuma ba jami’an ta bane.
KU KARANTA: Shugaban Nijar Bazoum Ya Taya Bola Tinubu Murnar Cin Zaɓe
Sanarwar ta tabbatar da cewa hukumar ta samu nasarar damke wani daga cikin masu yin aika-aikar a karamar hukumar Wudil tare da damka ma jami’an Yan sanda shi dan gudanar da bincike.
Daga nan hukumar ta kara jan hankalin al’umma da cewa su kauracewa duk wasu dake karbar kudi dan tabbatar da bayanan su kan batun kidaya a jihar Kano.