Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta umarci Bankin UBA “United Bank of Africa” da ya rike kudin Jihar Kano da ake zargin “DG Protocol” na gwamnan Kano wato Abdullahi Rogo da karkatarwa da yawansu ya kai naira miliyan dubu da miliyan 100 Daya.
Kotun karkashin jagoranci justis Emeka Nwite ta bada da umarnin ne bayan lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa da aikata almundana wato ICPC ya gabatar da bukatar Hakan.
Alkali ya yanke hukuncin cewa bukatar ta yi daidai kuma ya amince da ita.
KU KARANTA: Dan Majalisar Dokokin Kano Sarki Aliyu Daneji Ya Rasu
Ya kuma bayar da umarnin a buga umarnin kwace kudaden a cikin wata jaridar kasar nan don baiwa duk wani mai sha’awa damar bayyana a gaban kotun da kuma nuna dalilin da ya sa bai kamata a mika kudaden ga Gwamnatin Tarayya ba har abada.
An dage shari’ar har zuwa ranar 21 ga Janairu, 2026, don bayar da rahoton bin ka’ida.
An shigar da karar ne a ranar 3 ga Disamba kuma Z.S. Nass, Mataimakin Darakta a ICPC, ya shigar da ita a ranar 8 ga Disamba.
Hukumar ICPC na neman umarnin wucin gadi na kwace kudin Naira 1,109,230,000 ga Gwamnatin Tarayya, kasancewar kudin da ake zargin an samu ne daga ayyukan da ba bisa ka’ida ba.