• Sat. May 16th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Tsofaffun Leburorin Isiyaka Rabi’u a Rivers Sun Nemi Tallafin Iyalan Marigayin Da Gwamnatin Kano

BySani Magaji Garko

May 12, 2026

DAGA: NURA GARBA JIBRIN, KANO

Tsofaffun Leburorin hamshakin dan kasuwa kuma masananin Al’qur’ani Marigayi Sheik Isiyaka Rabi’u dake zaune a birnin Fatakol na Jihar Rivers sun roki Iyalan Marigayin da gwamnatin Jihar Kano da ta temaka musu sakamakon kunchin rayuwa da suka samu kansu a ciki.

Malam Ahmad Abdulmumin, jagoran Leburorin Isiyaka Rabi’u a cikin wani sakon murya da ya aikowa Wakilin Jaridar GLOBAL TRACKER ya ce sun sami kansu cikin kunchi na rayuwa, kuma mafi yawansu bama sa iya fita neman Abinci a garin da suke saboda shekaru sun cim musu.

Ya ce su ‘yan Asalin Jihar Kano ne, kuma iyalansu da suka haifa mafi yawansu a can suka haife su.

KU KARANTA: Manoman Albasu Sun Yi Allah Wadai Da Wahala, Barazanar Shugaban K/H Kan Biyan Diyyar Gonakinsu, Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Kano

“Tsakaninmu da Marigayi Sheik Isiyaka Rabi’u sai girmamawa da mutuntawa, ba bashi muke binsa ba, dukkan hakkokinmu lokacin da muke aiki a kamfaninsa na WAWUS ya biya mu, kai har wanda ma ba muyi aikin bama ya biya, to Amma yanayin kunchin rayuwa da muka samu kanmu a ciki sanadiyar shekaru da suka cimmana, da kuma yadda Allah ya Daukaka Iyalan Marigayin ne yasa muke neman temakonsu,” inji Ahmad Abdulmumin.

“A cikinmu akwai wanda aka yanke masa kafa, wasu daga cikin masu ma a gidan haya muke zaune, to yanzu abinda zamu ci ma wahala yake mana balle maganar kudin haya, Marigayi ya Kyautata mana, don Allah muna rokon Iyalansa da Allah ya daukaka su temakemu,” inji Shi.

Shugaban tsofaffun Leburorin ya kuma roki gwamnatin Jihar Kano karkashi jagoranci Injiniya Abba Kabir Yusuf da kuma masu kudi da sarakunan Kano da su temaka musu tare da kai musu dauki a rayuwarsu.

“Muna rokon masu kudi, mawadata, Sarakuna da Gwamnatin Jihar Kano da su temaka mana don kawo mana dauki a rayuwarmu,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *