Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Muhammad Sani na Biyu, ya rasu
A cewar majiyoyin fada, Mai martaba Sarkin ya rasu a birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya je domin duba lafiyat sa.
An haife shi a ranar 12 ga Disamba, 1942, marigayi Ahmed Muhammad Sani shine Sarkin Gumel na 16 ya rasu yana da shekaru 84.
Ya kasance daya daga cikin sarakunan gargajiya mafi dadewa a Arewacin Najeriya kuma mafi girmamawa.
Ya hau karagar mulki a ranar 16 ga Disamba, 1980, bayan rasuwar mahaifinsa.
Ya yi mulki na sama da shekaru 45.