• Mon. Sep 7th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Ba Wa Ministan Tsaro kwana 7 Ya Janye Kalamansa Kan Mahaifinmu Ko Mu Kai Kararsa Kotu — Iyalan El-Rufai

BySani Magaji Garko

Sep 7, 2026

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, sun bukaci Ministan Tsaro na Nijeriya, Christopher Musa, ya janye zargin da ya yi cewa El-Rufai ya taka rawa wajen shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar.

‎A cikin wata sanarwa da iyalan suka fitar a Abuja ranar Litinin, 7 ga Satumba, mai dauke da sa hannun Hon. Mohammed Bello El-Rufai, sun ce sun damu matuka da zargin da Janar Musa ya yi a yayin wata tattaunawa ta kai-tsaye da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today, ranar 3 ga Satumba.

‎A cewar iyalan, Ministan Tsaron ya yi zargin ne ba tare da gabatar da wata hujja da ke tabbatar da ikirarin nasa ba.

KU KARANTA: Kano Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Takalmin Taya Ta Farko a Nigeria 

‎Iyalan sun ce duk da cewa Musa yana da ’yancin bayyana ra’ayinsa, su ma suna da ’yancin neman a gabatar da sahihiyar hujja da za ta tabbatar da irin wannan zargi mai tsanani.

‎Saboda haka, iyalan sun ba Janar Musa wa’adin kwanaki bakwai daga ranar fitar da sanarwar, ko dai ya gabatar da hujjar da ke tabbatar da zargin, ko kuma ya janye kalaman nasa a bainar jama’a tare da ba da haƙuri, ta kafar da ya yi amfani da ita wajen yin zargin.

‎Iyalan sun yi gargadin cewa idan har ya gaza yin hakan, ba za su samu wani zaɓi ba illa su ɗauki matakin shari’a da ya dace a ƙarƙashin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *