• Thu. Sep 10th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Dan Takarar Gwamnan Kano a Jam’iyyar AP Ya Yi Allah-Wadai Da Kisan Gillar Da Aka Yi Wa Dan-Shagamu

BySani Magaji Garko

Sep 10, 2026

Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar Accord Party (AP) Ambassador Mukhtar Gashash, ya yi Tir da Allah Wadai kan kisan gillar da aka yi wa wani mai sharhi kan al’amuran siyasa a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, a unguwar Gaida da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

‎Ambassador Gashash ya bayyana kisan a matsayin abu mai matuƙar tayar da hankali da kuma ban tausayi, yana mai cewa lamarin ya kamata ya girgiza duk wani mai son zaman lafiya.

‎Ya ce bai kamata a halaka ɗan Adam saboda yana fadar ra’ayinsa ba, ya kamata a mutunta ra’ayin kowa tunda dokar kasa ta ba da dama kowa ya yi ra’ayin da yake ganin shi ya gamsu da shi.

KU KARANTA: Kano Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Takalmin Taya Ta Farko a Nigeria 

‎A sanarwar da Mai Magana da Yawun Dan Takarar, Gashash ya bayyana kisan a matsayin “mummunan aikin Ta’addanci kuma abin Allah-wadai ƙwarai da Gaske”

‎Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su Tsaurara bincike domin gano hakikanin abin da ya faru, da kuma gano waɗanda suka aikata kisan tare da gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

‎Rahotanni sun ce an kai wa Dan Shagamu hari tare da kashe shi a cikin gidansa da ke Gaida, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin damuwa tare da sake haifar da tambayoyi kan tsaron mutanen da ke amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana ra’ayoyinsu.

Dan Takarar Accord Party, ‎Ya kuma shawarci mazauna jihar da kada su ɗauki doka a hannunsu ko kuma su nemi ɗaukar fansa, sai dai su bai wa hukumomin tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *