DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO
Kungiyar masu hada-hadar kasuwancin manja da man Gyada dake Bello road kasuwar singa sun sha alwashin siyar da mansu cikin farashi mai sauki duba da alfarmar watan Ramadana da ake ciki da kuma karamar sallah dake tafe.
Shugaban kungiyar yan kasuwar Alhaji Fatihu Iliyasu ne ya sha alwashin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kasuwar singa dake Kano.
Ya ce kamata yayi yan kasuwa su yi amfani da wannan lokaci na azumi domin saukakawa alumma farashin kayayyakin masarufi da sauran kayayyakin bukata da alumma suke bukatar siya inda ya ce shi yasa yan kungiyar suke siyar da manja da man gyadar suka ga dacewar sanar da alumma sun rage farashin kudin manja da man gyada darajar Azumin watan ramadana.
Fatihu iliyasu wanda ya kwashe shekaru 22 yana sana’ar ya bayyana cewa, ya samu nasarori da dama a wannan sana’ar da kuma, koyawa matasa kasuwanci tare da yayesu domin cin gashin Kansu.
A don haka ya bukaci alumma da sauran masu bukatar manja da man gyada da su garzaya bello road domin Neman samu sauki da garabasa saboda falalar watan azimin Ramadan da kuma, karamar sallah dake tafe.
KU KARANTA: Sarkin Gaya Ya Nada Mujahid Bello Dagacin Gumakka
Shugaban ya shawarci yan kasuwa dake siyar da kayan masarufi musamman a wannan watan azumin Ramadan da su kasance masu tausayawa alumma wajen mu’amullar kasuwancinsu inda ya ce yin hakan zai karawa kasuwacinsu albarka.
Yace, wannan lokaci ne, na Neman lada da samun falalar Allah mahalicci da Neman Allah ya sanyawa harkokin kasuwanci albarka.
Haka zalika,yayi kira ga matasa da su kasance masu Neman sana’o’in dogaro da kai don kaucewa raina kananan sana,oi domin daga karamar sana,ace take zama babba, har a ci moriyarta yadda ya kamata.
Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta tallafawa kananan yan kasuwa da matasa da basu da sana’a wajen Samar musu da ayyukan da za su dogara da kawunansu domin kaucewa shiga munanan dabiu da basu kamata ba.