• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Da Dumi-Dumi: An Ga Watan Sallah a Saudia

ByGlobal Tracker

Apr 20, 2023

Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a yau Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023.

An ga watan ne a yankin Tumair na kasar Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana.

Hakan na nufin an kammala azumin watan a rana ta 29 ga Ramadan a kasar.

Gobe Juma’a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *