Zainab Musa Kwankwaso, ‘yar tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Rabiu Musa Kwankwaso, wadda kuma ita ce matar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ta shigar da ƙara a gaban kotu domin neman a raba aurensu, inda ta bayyana shirinta na mayar da sadakin da gwamnan ya biya a lokacin aurensu domin samun damar rabuwa da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa Zainab ta shigar da ƙarar ne a gaban Kotun Upper Area da ke Gudu, Abuja, inda ta nemi a raba aurensu ta hanyar tsarin Khul’i da shari’ar Musulunci ta tanada.
Takardar sammaci mai lamba CV/97/26 ta umarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya bayyana a gaban kotun a ranar 17 ga Nuwamba, 2026, domin amsa ƙarar da aka shigar.
A cikin bayanan ƙarar, Zainab ta bayyana cewa aurensu ya shiga mawuyacin hali sakamakon rashin kulawa, soyayya, ƙauna da kusanci tsakanin ma’auratan.
Ta kuma bayyana cewa ita ma ta rasa ƙauna da sha’awar ci gaba da zaman aure da gwamnan, lamarin da ta ce ya kai ga samun tsananin ƙin ci gaba da wannan zamantakewa.
Ta ƙara da cewa tana fargabar ci gaba da zaman auren a wannan yanayi zai iya sanya ta cikin mawuyacin hali wajen kiyaye dokokin Allah da sauke nauyin da ke kanta a matsayinta na matar aure.
A cewarta, duk ƙoƙarin da aka yi na sasanta su da dawo da zaman lafiya ya ci tura, yayin da ta bayyana cewa zuciyar gwamnan ta kauce daga wannan aure.
Saboda haka, ta bayyana a cikin takardun ƙarar cewa a shirye take ta mayar wa gwamnan sadakin da ya biya a ranar aurensu domin samun damar raba auren ta hanyar Khul’i. Wannan hanya ce da shari’ar Musulunci ta tanada wadda mace za ta iya bi domin neman rabuwa da mijinta, yawanci ta hanyar mayar da sadaki ko wani diyya da kotu ta amince da shi.
Rahotanni sun nuna cewa Zainab da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun yi aure ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, lokacin da take aiki a matsayin mataimakiyar mahaifinta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A Aurensu, sun haifj ‘ya’ya shida, yayin da Zainab take matsayin matar gwamnan ta biyu.
Lamarin neman sakin ya zo ne a daidai lokacin da dangantakar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da surukinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta samu matsala, musamman bayan gwamnan ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Sai dai babu wata tabbatacciyar hujja da ke nuna cewa wannan saɓanin siyasa ne ya zama dalilin da ya sa Zainab ta shigar da ƙarar neman saki, domin dalilan da aka bayyana a cikin takardun kotun sun fi mayar da hankali kan matsalolin zamantakewar aurensu.
A halin yanzu, ana jiran matakin da kotun za ta ɗauka bayan sauraron ɓangarorin biyu, yayin da har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ba a samu cikakken martanin Gwamna Abba Kabir Yusuf ko gwamnatin Jihar Kano kan ƙarar ba.