• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC

ByGlobal Tracker

Feb 10, 2023

Zauren Bada Shawarwari na jam’iyun Siyasa na kasa reshen jihar Kano ya ce ko dai a Dena Kashe Mutane a lokacin da jam’iyun Siyasa ke gudanar da Gangamin Yakin Neman zabe ko kuma ya dauki matakin hana zaben ta hanyar kaurace masa da kuma Jan hankalin mutane su kauracewa zaben don tsira da rayukan su.

Matemakin shugaban Zauren Alhaji Isa Nuhu Isa ne ya bayyana hakan a Taron manema labarai a Kano dake arewa maso yammacin Nigeria.

Isah Nuhu wanda kuma shine shugaban jam’iyar Zenith-Labour Party ya ce abin takaici ne yadda manyan Yan Siyasa da ‘Yan takara suna kallo ana kashe mutane amma sunyi kunnen uwar shehu saboda basu damu da rayukan mutane ba.

Ya ce abin takaici ne yadda duk da tsarin da akayi da rundunar Yan sanda ta jihar Kano da matemakin sifeton Yan sanda ta kasa Mai kula da shiyya ta daya dake nan Kano kan yadda kowanne Dan takara sai ya nemi sahalewar rundunar wajen gudanar da gangamin yakin neman zabe Amma ake cigaba da kashe mutanen da wasu ma basuji ba basu Gani ba, kuma a bainar jama’a wasu ma manyan Yan siyasar suna gani abubuwan da suke faruwa amma sunki cewa komai saboda Babu ‘ya’yan su a ciki.

Matemakin shugaban yayi barazanar cewa zauren zai daukaka maganar har zuwa gaban babban sifeton Yan sandan Nigeria ko gaba da can domin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma gorantawa matasa da suke bari ana amfani da su wajen tayar da hargitsin zabe, yana mai cewa dukkan ‘yan siyasar suna killace ‘ya’yan su tare da bawa ‘ya’yan talakawa kayan maye da makamai domin tayar da hankali ko ma kashe mutane, wanda shine babban abin takaicin a cewar Isah Nuhu.

“Matukar kwamishinan Yan sanda jihar Kano bai dauki mataki ba wallahi Zamu tafi har gaban babban sifeton Yan na kasa saboda mun daura damba, garin nan namu ne, ‘ya’yan mu ake kashewa, garin mu idan ya lalace, kasuwancin da ake lalatawa namu ne”, inji Nuhu Isah.

“Kuma idan abin bai dena ba zamu hana yin zaben, zamu hana mutane ko jam’iyu su shiga zaben, matukar kana da kishin Kano zamu tattauna da Kai karkashin jagorancin wannan kungiya kuma zamu hana ka shiga zaben matukar mahukunta basu dauki matakin dena kashe mutane ba,” inji Nuhu Isah.

One thought on “Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *