Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da su zauna lafiya a lokutan babban zabe na kasa da za’a gudanar a gobe Asabar.
Mai Martaba Sarkin yayi kiran ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi na musamman ga manema labarai a fadarsa.
Cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya fitar ta ambato Ado Bayero na cewa sai da Zaman lafiya ne ake iya aiwatar da komai, a don haka ne ya bukaci matasa su kaucewa furta munanan kalamai da amfani da muggan makamai tare da shan kayan maye da dukkan wani abu daka iya jirkitar da hankalin su domin kaucewa abubuwan da basu kamata ba.
KU KARA TA: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano
Sarkin ya sake jaddada bukatar Hakimai da Dagatai da masu unguwanni su cigaba da wayar dakan al’umarsu muhimmacin Zaman lafiya.
Yayi kira ga jami’an tsaro dasu cigaba dasa ido akan dukkan wanda ya aikata wani lafi tare da hukunta shi.
Aminu Ado yayi addu’ar samun zabin shugabanni na gari a dukkan matakan zabubbukan da za’a gudanar a fadin kasar nan.