• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

AU Ta Gamsu Da Shirin Nigeria Na Gudanar Da Sahihin Zabe — Kenyyata

ByGlobal Tracker

Feb 24, 2023

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce ta gamsu da shirin gwamnatin Nigeria na gudanar da sahihin zabe da zai zama karbabbe ga kowa.

Wakilin kungiyar kuma tsohon shugaban ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya shaida wa BBC cewa ya ga zimmar da gwamnatin Najeriya ke da ita na ganin an gudanar da sahihin zaɓuka.

Mista Kenyatta ya ce alamu sun nuna cewa hukumomi suna da ƙwarin gwiwar cewa za su iya gudanar da zaɓuka masu gaskiya a ranar Asabar.

KU KARANTA: ZABE: Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro
An samu rahotanni da dama na sayen kuri’u da kuma cin hanci da rashawa a rumfunan zaɓe a zaɓukan da suka gabata.

Ana kuma ƙara samun tashin hankali, inda aka kashe ɗan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar Labour a ranar Larabar da ta gabata a jihar Enugu.

An harɓe Oyibo Chukwu tare da ƙona gawarsa a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

KU KARANTA: Zaben 2023: Masu Yi Wa ƙasa hidima Ne Za Su Yi Aiki da BVAS – Shugaban INEC
Mista Kenyatta ya yi gargadin cewa za a fuskanci kalubale, amma ya ce ‘yan takarar shugaban kasar na tunanin za su iya “warware” matsalolin da suka hada da matsalar tsaro da kuma karancin kudi a Nigeria wadanda suka haifar da rikici a ‘yan makonnin da suka gabata.

Mista Kenyatta ya yi gargaɗin cewa za a iya cin karo da matsalolin, amma ya ce ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa na ganin za su iya magance matsalolin.

Ya ce zaben Najeriya yana da muhimmanci saboda ita ce ƙasa mafi girma a nahiyar Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *