• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kano: Hanyarmu Ta Zama Barazana Ga Rayuwarmu — Al’ummar Dan-dishe

BySani Magaji Garko

Sep 15, 2024

DAGA: SANI IDRIS MAI-WAYA RIJIYAR LEMO, KANO

Al’ummar unguwar Dan-dishe dake yankin Karamar hukumar Ungogo sun roki gwamnatin jihar Kano ta kawo musu dauki Sakamakon barazana da hanyar yankin ta zamewa mutane saboda lalacewarta.

Yayin tattaunawarsa da manema labarai, wani mazaunin yankin Auwal Lawan ya ce mutane na shan bakar wahala gami da fuskantar barazana ga lafiyar su sakamakon lalacewar hanya.

“Yankin nada matukar yawan al’umma sosai, amma rashin hanya yana barazana ga lafiyarsu, muna kira gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da ta kawo mana dauki,” inji Auwal.

KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Zamu Girmama Shawarwarin Yan Kasuwar Kano — Shugaban REMASAB

“Ruwa ya zaizaye hanyar gaba daya, wannan abun yafi karfinmu, muna rokon masu ruwa da tsaki da su kawo mana dauki,” inji shi.

Auwal Lawan daga nan ya bukaci shugaban karamar hukumar Ungogo da ‘yan majalisun yankin Sanatan Kano ta tsakiya dama gwamnatin jihar Kano da su kai musu dauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *