Sa’o’i kadan bayan rantsar da shi, sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hanu a kan dokar dakatar da dukkan tallafin da kasarsa take bawa kasashen duniya ba tare da amfanar tallafin ta kai staye ba.
Cibiyoyin bibiya da ba da tallafi sun bayyana cewa Amurkan ta bada tallafi da ya kai dala biliyan 60 a shekarar 2023.
Kasar Ukraine ce a kan gaba a jerin kasashe 20 da suke samun tallafi daga Amurka kuma masana na ganin sune kasashen da tsuke bakin Aljihun da shugaban Amurka Donald Trump yayi zai fi shafa.
KU KARANTA: Zan Haramta Wa Duk Yaran Da Aka Haifa A Amurka Izinin Zama Yan Kasa — Donald Trump
A 2023 Ukraine ta karbi tallafin kusan dala biliyan 14 da rabi daga hukumar bunkasa kasashe masu tasowa ta kasar Amurka USAID.
Jordan ce ta biyu a tallafin kudaden na Amurka inda ta karbi dala miliyan 770 sai Yemen mai kusan dala miliyan 360 yayin da Afghanistan ta karbi dala miliyan 332.
A tallafin kayan yaki kuma Israel ce ke kan gaba.
Ga jerin kasashe 20 da tallafin da Amirka ta basu a 2023:
Ukraine: $16.62bn
Israel: $3.31bn
Ethiopia: $1.77bn
Jordan: $1.72bn
Egypt: $1.45bn
Afghanistan: $1.27bn
Somalia: $1.21bn
Nigeria: $1.01bn
DRC: $0.98bn
Syria: $0.9bn
Kenya: $0.89bn
Yemen: $0.83bn
South Sudan: $0.79bn
Uganda: $0.71bn
Colombia: $0.71bn
Mozambique: $0.66bn
Tanzania: $0.65bn
Lebanon: $0.64bn
Iraq: $0.59bn
Bangladesh: $0.55bn.