Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta kasa INEC ta dage fara Karbar Sakamakon Zaben Shugaban Kasar Nigeria da aka gudanar a Asabar din nan zuwa Gobe Litinin.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a Abuja.
Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne bayan gabatar da sakamakon jihar Ekiti a zauren tattara sakamakon zaben shugaban kasar da ke Abuja babban birnin Nigeria.
KU KARANTA: Bawa NHFSS Damar Samar Da Tsaro a Lokacin Zabe Zai Kara Mana Karfin Gwiwa — Abdullahi Al-ameen
Shugaban na INEC ya ce kasancewar jihar Ekitin ce kadai ta kai sakamakonta zuwa zauren tattara sakamakon zuwa yanzu, hukumar ta dage karbar sakamakon zuwa ranar Litinin da misalin karfe 11:00 na safe.