Sabon sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte ya ce a yanzu babu maganar yiwa kasar Ukraine rejista a kungiyar, yana mai cewa ‘a yanzu babu yiwa Ukraine a teburin NATO.’
Mark Rutte ya bayyana hakan ne a tattaunawa da wani gidan talabijin wanda Dan jarida Mai bibiyar harkokin yaki Megatron ya tabbatar.
Ya ce yakamata kungiyar da dai-daita alakar kasashe mambobin kungiyar da kasar Rasha.
KU KARANTA: Yakin Rasha Da Ukraine: A Shirye Nake Na Tattauna Da Putin — Zelensky
Wannan na zuwa yayin da ake cigaba da yaki a yankin Kursk na Ukraine, inda rahotanni suka ce sojojin Rasha sun zagaye na Ukraine, inda ake fargabatar Rasha ka iya gamawa da sojojin Kyiev.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Amurka Donald Trump ya roki shugaban Rasha Vladimir Putin cewa kada Moscow ta gama da sojojin Kyiev inda Putin ya ce zata mutunta sojojin matukar suka jinge makamansu.
A baya dai Putin ya bayyana ka’idoji uku da yakamata a cika su kafin a tsagaita wuta ko jingine makamai wanda suka hada: ka da NATO ta yiwa Ukraine rejistar shiga kungiyar, baza a girge jami’an kwantar da tarzomar NATO a Ukraine ba, dukkan yankin da Rasha ta mamaye zasu zama baza a mayar da su zuwa Ukraine ba sai dai su kasance a Rasha ciki harda yankin Crimea.
Hakazalika, Rasha ta ce babu maganar tsagaita wuta ta wani dan lokaci sai dai a dena yakin gaba daya da kuma tabbatar da zaman lafiya ga kowanne bangaren.