• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Babu Hanun Khamisu Ahmed A Gazawar Haruna Aliyu Zuwa Gasar Nahiyar Afirka — ‘Mailantarki Care’

BySani Magaji Garko

Apr 23, 2025

DAGA: ZAHARADEEN SALEH, KANO

Kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki care dake birnin tarayyar Abuja, ta musanta zargin da jami’in tsare tsare na kungiyar flying eagles ta kasa Abubakar dan fulani yayi akan shugaban kungiyar Mailantarki, Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki akan yana da hannu wajen hana tafiya da dan wasan kungiyar Haruna Aliyu, gasar kasashen nahiyar afrika ta Yan kasa da shekaru ashirin wadda zai gudan a kasar masar.

Daraktan yada labarai na kungiyar Adamu Usman Ahmed, ne ya musanta zargin a wata sanarwa daya fitar mai dauke da sa hannu sa, a inda ya ce wannan labari da Abubakar Dan Fulani, bashi da tushe ballanta na makama.

Sanarwar ta kara da cewa mun samu labarin jami’in flying eagles Abubakar Dan Fulani yayi hira a gidan Rediyon Amana dake jihar Gombe, yana yiwa Honarabil Khamisu Ahmed Mailantarki kazafin shine ya hana Haruna Aliyu ya shiga cikin tawagar kungiyar kwallon kafa ta flying eagles ta Nigeriya bisa dalilin korafi daya mika wa hukumar kwallon kafa ta kasa, a cewar Abubakar Dan Fulani.

KU KARANTA: Tsohon Dan Wasan Barcelona da Arsenal Cesc Fabregas ya yi Ritaya Daga Kwallon kafa

Adamu Usman ya ce Dan Fulani yana so ne yayi amfani da damar sa ne ya bata sunan shugaban kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki saboda dukkan su sun fito ne daga jihar Gombe, tare da kalamai masu dauke da bace masu kama dana siyasa duba da cewa Mailantarki jigo ne a jamiyyar adawa a jihar ta Gombe.

Haruna Aliyu wadda kawo yanzu dan wasan Doma United ne amma tunin ya sanya hannu a hukumance a wata takarda a kungiyar ta Mailantarki hakan ya bashi damar zama dan wasan kungiyar da zarar karshen kakar gasar kwararru aji na biyu wato NNL tazo karshe nan da yan watanni, amma daga bisani dan wasan ya sake saka hannu a wata kungiyar wadda hakan ya saba doka.

Duba da irin yadda dan wasan Haruna Aliyu ya jefa kansa a rikita-rikita tare da biye wa gurguwar shawara sakamakon halin da Abubakar (Yellow) ya tsunduma shi ne ya sake kulla yarjejeniya da wata kungiyar, bayan tunda farko yana da yarjejeniya daya kulla da kungiyar Mailantarki kamar yadda daya daga cikin jami’in kungiyar Mailantarki Auwal Kawuwa ya tabbatar da hakan a hirar sa na mayar da martani tare da gidan Rediyon Amana dage Gombe, hakan ne yasa aka cire sunan dan wasan wadda hukumar kwallon kafa ta kasa tayi, duba da ita hukumar tana sane da yarjejeniyar da dan wasan ya kulla da Mailantarki daga farko, sannan daga bisani ya kuma sanya hannu a wata kungiya ta daban a baya-baya nan yayin da suke karbar horo a sansani atisaye din kungiyar Flying eagles ta domin tunkarar gasar nahiyar afrika ta yan kasa da shekaru 20.

Khamisu Ahmed shine mai kungiyar Mailantarki kuma mutum ne mai son cigaban Yan wasan jihar Gombe, da kuma Arewacin Nigeria da baki daya.

Dan wasan Haruna Aliyu ya kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki care a kakar wasa ta shekara 2024 zuwa 2025 a gasar ajin kwararru ta kasa, ya ce har yanzu Haruna Dan wasan kungiyar Mailantarki har sai an kammala kakar wasa ta bana amma Kuma ya Kara Sanya hannu a wata kungiyar.

A karshe kungiyar kwallon kafa ta Mailantarki Care FC tayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da suyi watsi da labaran yarfe da Abubakar Dan Fulani ( Yellow) yake yadawa akan shugaban kungiyar Mailantarki Care FC Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki.

Yan wasan kwallo da dama ne daga jihar Gombe hada da sauran jahohin arewa da Nigeria baki daya samu gagarumar dama karkashin daukar nauyin shugabar guniyar Mailantarki Care FC, inda wasu sukayi nasarar samu kulob a nahiyar turai wasu Kuma sun dawo suna cigaba da karbar horo na musamman kafun su koma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *