• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Badakala Ce Ta Sa Aka Kori Baffa Bichi Daga Sakataren Gwamnatin Kano Ba Rashin lafiya Ka Dai Ba — Waiya

BySani Magaji Garko

May 2, 2025

Gwamnatin Jihar Kano ta kalubalanci tsohon sakataren gwamnatin jiha Alhaji Baffa Bichi da ya fito ya bayanan abinda yake da shi wanda aka aikata cin hanci da rashawa ko aikata ba dai-dai ba, tana mai cewa “Badakala ce ta sa aka Kore shi ba rashin lafiya ka dai ba.”

Gwamnatin ta ce tana da bayanai na badakalar kudi da yayi a ayyukan sa a gwamnatin jihar Kano da hukumar Bada tallafin karatu ta gwamnatin tarayya TETFUD wacce hakan ta sa aka kore shi daga aiki.

Kwamishinan ƴan labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya yi kalubalen a taron manema labarai a nan Kano ranar Juma’a da yamma.

KU KARANTA: Zakka, Hubusi, Wakafi Da Yadda Zamu Inganta Rayuwar Al’ummar Kano — Barista Dan Almajiri

“Kada tsohon sakataren gwamnatin ya manta cewa ba rashin lafiyar sa ne kawai yasa aka kore shi daga sakataren gwamnati ba, harma da badakalar karkatar da Shinkafa da makusantansa suka yi wanda ana ganin yana ma da hanu a ciki,” inji Waiya.

“Tunda aka kirkiri Jihar Kano ba’a taba yin gwamnatin jiha a Kano da ta yi Al’mundahana da wawure dukiyar al’umma kamar gwamnatin APC ta shekaru 8 a jihar Kano ba, Amma wai Baffa Bichi da ya saka yaransa suka wawure dukiyar al’umma shine zai ce yana da bayanan da wasu suka aikata ba dai-dai ba,” inji Waiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *