Jaridar “A. G. D. Only TV” ta karrama shugaban karamar hukumar Ghari dake Jihar Kano Alhaji Hashim Garba Mai-sabulu a matsayin daya daga cikin jajirtattun shugabanni kananan hukumomin Kano da suke gudanar da ayyukan cigaban al’umma.
Shibili Rabi’u Sabon-titi, jami’in yada labarai na karamar hukumar ta Ghari wacce aka fi sani da Kunchi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER.
Sanarwar ta ce mamallakin Jaridar Abubakar Gambo Dauda shine ya jagorancin bikin miqa kyautar girmamawar ga shugaban a sakatariyar karamar hukumar.
Shugaban jaridar ya ce sun zabo Mai-sabulu ne a cikin shugabannin Kananan hukumomi 44 la’akari da irin ayyukan da yake gudanarwa na raya kasa a yankin karamar hukumar.
“Mun karrama Mai-sabulu ne la’akari da irin ayyukan cigaban al’umma tin daga kan samar da ruwan sha da bunkasa Ilimi da harkokin lafiya da gyaran titina da sauran bangarori,” inji shugaban jaridar.
A lokacin da yake karbar lambar girmamawar, Hashimu Garba Mai Sabulu ya bayyana jin dadi da godiyarsa ga jaridar bisa zabo shi da tayi har aka bashi lambar yabo.
Ya kara da cewa hakan zai qara musu Kaimi wajen ci gaba da aiyukan raya kasa ga al’ummar yankin.