• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mako Biyu Kafin Babbar Sallah, Dabbobi Na Araha a Kebbi

BySani Magaji Garko

May 26, 2025

A dai-dai lokacin da ya rage saura mako biyu, Musulmai su gudanar da Bukukuwan Babbar Sallah, farashin Dabbobi a kasuwanni a Jihar Kebbi nada sauki.

Wakilin GLOBAL TRACKER a Jihar Kebbi, ya shiga kasuwanni inda ya ruwaito cewar, farashin raguna, tumaki da awaki wadanda suka Isa yin layya na da sauki saboda suna iya sayuwa.

A kasuwar Ambursa da Argungu da Dodoro, ana iya samun Rago daga naira 100,000 zuwa naira 450,000; sai Tunkiya daga naira 70,000 zuwa naira 250,000 haka zalika Awaki daga naira 50,000 har zuwa naira 250,000.

KU KARANTA: A hir Din Kungiyar CAN Da Yiwa Musulmi Kutse A Addininsu — Yusuf Dingyadi 

Wasu masu Saida dabbobin, Malam Musa Ambursa da Malam Shehu Adamu sun bayyana cewar a sallar bara dabbobi sunfi kudi idan ka kwatanta da bana.

Shi yasa suka ce, har idan babbar Sallah ta gabato zuwa makon gobe ga kuma biyan maa’ikatan gwamnati albashi to sai abin da farashin dabbobi ya tsaya inda suka bada shawara cewar matukar mutum nada kudinsa, ya harzanta sayen dabbobinsa ba sai lokaci ya kure ba.

Wasu da suka zo sayen dabbobin, sun sheda cewar, dobbobi na da sauki a yanzu kafin ayi albashi don haka suna fatan atafi a haka zuwa sallah.

Sun roki Yan kasuwa da su saukakawa al’umma domin samun lada gurin Allah da kuma habakar dukiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *