Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma shugaban Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, yana duba yiwuwar shiga kawancen adawa kafin babban zaben 2027, in ji Arise News.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben 2027 da kuma aniyar ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, tare da yawancin ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano, zuwa Jam’iyyar APC mai Mulkin Nigeria.
Majiyoyi sun ce Kwankwaso yana tattaunawa da ADC kan yiwuwar kawance da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Mista Peter Obi.
KU KARANTA: Kwankwaso a 69: Mai Hangen Nesa, Jigo a Siyasar Arewa… Ya Kawo Abba Don Cigaban Kano – Bakwana
A cewar majiyoyin, ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar Kwankwaso ya shiga ADC tare da membobin kungiyar Kwankwasiyya da magoya bayansa na siyasa.
Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa a hankali yayin da ‘yan siyasa ke binciken kafa wani kawancen adawa kafin zaben 2027.