• Sat. Apr 11th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

DA DUMI-DUMI: Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Shirin Tsige Matemakin Gwamna

BySani Magaji Garko

Mar 5, 2026

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara shirin tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Kwamared Aminu AbduSalam Gwarzo, ta hanyar aike masa da takarda wacce ta kunshi zarge-zargen da ake yi masa na aikata laifukan da za su iya bada dama a tsige shi.

A zaman majalisar na musamman da aka yi a yau Alhamis, sanarwar da aka karanta a zaman majalisar ta kunshi zarge-zargen rashin da’a, cin zarafin mukamai da kuma keta amanar jama’a.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Lawan Husaini, wanda ya yi wa manema labarai jawabi bayan zaman, ya tabbatar da lamarin, ya ce ya gabatar da sanarwar tsige shi.

Ya ce ‘yan majalisar 38 ne suka sanya hannu kan takardar tuhumar da ake masa…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *