• Sat. Nov 14th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Yabawa Gwamnan Kano Bisa Cire Waiya Daga Kwamishinan Yada Labarai — Kwararren Dan-jarida

BySani Magaji Garko

Nov 1, 2026

Kwararren Dan jarida a Jihar Kano da ma Nigeria ba ki daya Dakta Garba Ubale Danbatta ya Yabawa Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf bisa cire tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya daga mukamin Kwamishinan Yada Labarai.

Cikin wani sako da Dakta Garba Ubale Danbatta ya aikowa ‘yan Jaridu ya ce abubuwan da tsohon Kwamishinan yayi sun fi kama da ayyukan kungiyoyi maimakon aikin jarida da kuma daga darajan fanin a fadin Jihar Kano.

“A matsayin mu na wanda suka shafe fiye kimanin shekaru 30 muna aikin Jarida, muna yabawa Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusif da matakin daya dauka na cire tsohon kwamishinan yada labarai daga kujerar sa, saboda kusan ba aikin jarida yayi tayi ba, aiki yayi tayi irin na yan gwagwarmaya wanda hakan kusan a iya cewa kwamacala ce, domin yaci karo da sharruda ko kaidoji aikin Jarida,” inji Dakta Danbatta.

KU KARANTA: Kotu Ta Aike Ta Masu Ta’ammali Da Ajiyar Kayan Maye Gidan Gyaran Hali Na Shekaru 2 a Kano — Kwamitin Kar-ta-Kwana

“Irin abubuwan da ya rika ya jawowa Jihar Kano mummanar fahinta da suka daga kungiyoyin dake sa ido akan harkar aiki jarida da kuma hakkin yan jarida, abun babu dadin ji,” inji shi.

Dakta Garba Ubale Danbatta yayi fatan mai girma Gwamna wannan karon zai ajiye kwarya a gurbin ta, waje nada wanda ya cancanta kuma yake da kwarewa akan aikin jarida da kyakykyawar mu’amullah da yan jarida domin kawo gyara a aikin, tare da dawo martabar aikin jarida a Jahar Kano.

“Matukar gwamnan Kano ya yi mana haka, mu kuma a shirye muke muci gaba da bada dukkan wata gudummawa da shawarwari da zata taimaka wajen kyautata aikin tare da daga darajar sa a Jihar Kano a idon Duniya,” inji Danbatta.

Garba Ubale Danbatta dai ya shafe sama da Shekaru 30 Yana aikin jarida a ciki da wajen Nigeria.

Dakta Danbatta yayi aiki da Sashen Hausa na DW Hausa dake Birnnin Bonn a kasar Germany, yayi aiki a Sashen Hausa na Daily trust, yayi mataimakin Editor na Jaridar Rariya, yayi Editor na Hamada Radiyon dake Abuja, yayi shugaban Sashen Hausa na gidan Radiyon Kiss FM dake Abuja, kafin ya koma Radio Nigeria a matakin Manager.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *