• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Jam’iyar NNPP Kawai Na Ce a Zaba — Kawu Sumaila

ByGlobal Tracker

Mar 11, 2023

Zababben sanatan Kano ta Kudu, Honarabil Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana marawa wata jam’iyya baya a zaben gwamna da ke tafe, inda ya ce jam’iyar NNPP kawai ya ce a zaba.

Mataimaki na musamman ga zababban Sanata Sumaila kan harkokin yada labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano, inda ya ce Abba K. Yusuf da dukkan Yan takarar jam’iyar NNPP a matakin majalisar jiha Kawai kawu ya ce a zaba.

Abbas yace labarin da ake yadawa ba shi da tushe ballantana makama.

Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yada labarin na bogi, inda yace a shirye su ke su dauki matakin shari’a kan duk mutumin da ke neman bata sunan Kawu Sumaila.

KU KARANTA: YANZU YANZU: Kawu Sumaila Ya Ci Zaben Sanatan Kano ta Kudu

Ya ce Sanata Kawu Sumaila cikakken mai biyayya ne ga jam’iyyar NNPP da jagoranta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a don haka ba zai taba furta kalaman da ke nuni da a zabi wata jam’iyya ta daban ba a yayin zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiha.

Abbas ya rawaito Sanata Kawu Sumaila na kira ga daukacin al’ummar jihar Kano da su zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano tare da sauran ‘yan takarar majalisar jiha a tutar jam’iyyar NNPP a zaben da zai gudana a ranar 18 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *