• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Jam’iyyar NNPP ta Lashe kujerar Majalisar Jiha ta Karamar Hukumar Rano

ByGlobal Tracker

Mar 19, 2023

Jam’iyyar NNPP ce ta lashe kujerar Majalisar dokokin jihar Kano ta karamar hukumar Rano Kuma ta samu Rinjaye a Sakamakon Zaben Gwamna da akai jiya Asabar.

Jami’in tattara Sakamakon da hukumar ta tura farfesa Adamu ne ya bayyana hakan yayin sanar da Sakamakon karshe na Zabukan a cibiyar tattara Sakamakon zabe ta karamar hukumar Rano..

Ya bayyana Muhammad Ibrahim Malami na NNPP a matsayin Wanda ya samu kuri’u mafiya Rinjaye a matsayin Sabon Dan majalisa da yawan kuri’u dubu 18 da Dari 7 da doriya.

KU KARANTA: Ku Guji Ta da Hargitsin Siyasa, Mai Unguwar Tukuntawa Ga Al’ummar Kano.

Sai Kuma Nura Dallami Dan majalisar me ci yanxu na APC yazo na biyu da yawan kuri’u dubu 15 da doriya.

Tuni wakilin Kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai ta kasa Kabiru Alhassan Rurum Wanda shine jami’in karbar Sakamakon na Jam’iyyar NNPP a karamar hukumar ya taya sabon Dan majalisar da Kuma Dan takarar Gwamnan Abba Gida Gida murnan nasara da sukai a karamar hukumar Rano tare da fatan samun makamanciyar ta a sauran kananan hukumomin Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *