• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zaben Gwamna a Nigeria: Jihohin Da APC, PDP, NNPP Suka Yi Nasara

ByGlobal Tracker

Mar 21, 2023

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta samu nasarar cinye kujerun gwamna guda goma sha biyar (15) a sakamakon da aka bayyana kawo yanzu a zaɓen ranar Asabar 18 ga wata da aka gudanar a faɗin jihohin ƙasar nan 28.

Yayin da jam’iyyar PDP babbar mai hamayya ta samu kujerun gwamna takwas (8), sai kuma Jam’iyyar NNPP wadda ta samu kujerar gwamna ɗaya.

Jam’iyyar APC ta samu nasara a jihohin Sokoto da Katsina da Jigawa da Gombe da Lagos da Kwara da Niger da Yobe da Nasarawa da Cross Rivers da Ebonyi da Ogun da Benue da Kaduna da kuma jihar Borno.

Sai kuma jam’iyyar PDP da ta samu nasara a jihohin Plateau da Bauchi da Oyo da Delta da Rivers da Akwa Ibom da Zamfara da kuma jihar Taraba.

Sai jam’iyyar NNPP da ta samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Kano.

KU KARANTA: Jigo a NNPP Sagir Koki, Ya Taya Abba Gida-gida Murnar Lashe Zabe

Haka kuma hukumar zaɓen ta dakarar karɓar sakamakon jihohin Abia da Enugu, saboda rashin jituwa da aka samu tsakanin wakilan jam’iyyu a wasu ƙananan hukumomi.

Sannan kuma hukumar ta INEC ta ayyana sakamakon jihohin Kebbi da Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *