Sakataren jam’iyar NNPP na Karamar hukumar Ungogo ya taya zababban gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf Murnar Lashe zaben yana mai bayyana sakamakon zaben a matsayin nasara ga al’ummar jihar Kano.
Honarabil Shafi’u Hussain Kura ya bayyana hakan a tattaunawarsa da GLOBAL TRACKER.
Ya ce al’ummar Ungogo zasu amfana da sabbin tsare-tsaren sabuwar Gwamnatin ta NNPP la’akari da irin cigaban da tsohuwar Gwamnatin Injiniya Dakta Rabi’u Musa kwankwaso ta kawo a jihar Kano, yana mai cewa sabuwar Gwamnatin zata zama cigaban tsohuwar Gwamnatin ta fannin ayyukan raya kasa.
KU KARANTA: Zaben Gwamna a Nigeria: Jihohin Da APC, PDP, NNPP Suka Yi Nasara
Yayi fatan al’ummar jihar Kano za su rika yiwa Gwamnatin addu’ar cigaba domin samun Nasarar gudanar da ayyukan alkhairin da cigaban rayuwar Mutanen Kano.
“Gwamnatin Injiniya Abba Kabiru Yusuf zata bunkasa ilimi musamman Kai dalibai kasashen waje da lafiya da bunkasa Kasuwanci, kowa ya san cewa Kano garin Kasuwanci ne, to saboda haka Gwamnatin mu zata bunkasa kasuwar al’ummar jihar Kano”, inji Shafi’u.
Ya ce “muna so al’umma su rika yiwa Gwamnatin mu addu’o’in gudanar da ayyukan da mutane zasu amfana, muna fatan za’a çigaba da Taya Injiniya Dakta Rabi’u Musa kwankwaso addu’ar zama shugaban kasar Nigeria, domin matukar madugu ya zama shugaban kasa al’ummar Kano za su dara.”