• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ba Zan Yi Wa Sabon Gwamnan Kano Katsalandan Ba – Kwankwaso

ByGlobal Tracker

Mar 31, 2023

Madugun Jam’iyar NNPP kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya wuce a Najeriya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi wa gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, katsalandan cikin harkokin mulkinsa ba.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa, wanda kuma shine ubangidan zababben gwamnan Kanon wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida a siyasance, ya ce idan gwamnan mai jiran gado ya nemi shawararsa, zai ba shi.

Wasu mutane sun yi ta nuna fargabar cewa ba lallai ne Abba Kabir Yusuf ya samu cikakken ikon tafiyar da gwamnatin Kano ba, idan an rantsar da shi, saboda mai yiwuwa Kwankwaso zai yi ta ba shi umarni da yi masa katsalandan.

KU KARANTA: Yan Kasuwa a Ungogo Sun Ta Ya Abba K. Yusuf Murnar Lashe Zabe

Sai dai, yayin wata tattaunaw da BBC Hausa, tsohon gwamnan na Kano, ya ce a matsayinsa na ɗan Kano zai riƙa ankarar da gwamnatin wadda za a rantsar a ƙarshen watan Mayu, duk lokacin da ya ga ta kauce hanya.

Ya ce “Ai shi mulki ko mai shararka ne, ka ba shi, to ka koma waje ɗaya in ya nemi shawararka ka bayar, idan kuwa bai nema ba, sai ka yi shiru.”

“A lokacin da nake gwamna a Kano, da su Abba aka yi mulkin, su ne suka taimaka na cimma nasarar da ya samu”, in ji Kwankwaso.

Kwankwaso ya ce, “ a yanzu na tabbata shirmen da Ganduje ya yi a Kano, ai Abba ya wuce wannan.

Saboda haka ne ma, muka zauna muka duba dukkan mutanen namu muka ɗauki wanda muke ganin idan Allah ya yarda in dai irin matsaloli na Ganduje ne ba za a samu ba.”

KU KARANTA: Murtala Kadage na NNPP Ya Lashe Zaben Dan Majalisar Jiha na Garko

Tsohon gwamnan, ya ce,” Dukkanninmu a jihar Kano muna farin ciki Allah ya fitar da su, kuma muna addu’ar Allah ya raka taki gona.”

A cewar Kwankwaso, abin da yake so a sani shi ne ”ko wane ne yake mulkin Kano, ko soja ko ma wane ne, to ba za mu kyale shi, ya yi rashin kyautawa ba.”

“Don haka ko Abba ne ke mulki ko ma waye duk wani abu da yake daidai za mu faɗa masa, idan ma ba daidai ba ne za mu faɗa.”

Kwankwaso ya ce, shi abin da ya sani, shi ne za a gyara duk wasu abubuwa da aka yi ba daidai ba, a lokacin gwamnati mai barin gado.

Ya kuma ce, za su yi hakan ne don a gyara Kano ta yi kyau.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *