• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rantsar Da Sabon Gwamnan Kano: KAROTA Zata Girke Jami’an ta 1,000

ByGlobal Tracker

May 27, 2023

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Karota ta ware jami’anta guda dubu daya (1,000) da za su kula da zirga-zirga ababen hawa a ranar rantsar da Sabon Gwamnan Kano injiniya Abba Kabiru Yusuf.

Mai riƙon shugaban Hukumar, kuma Daraktan Mulki Alhaji Abdullahi Yahuza ne ya bayyana hakan inda ya ce za’a zuba jami’an KAROTA ne domin kula da kaiwa da kawowar ababen hawa

Haka kuma, za a rufe wasu daga cikin titinan da suka shafi kewayen filin da za’a gudanar da taron.

KU KARANTA: ‘Mariya Bunkure, Kwararriya Mai Kishin Ilimi a Kano’ — Dahiru Adda’u

Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Naisa ta ja hankalin jami’an da su gudanar da ayyukan su cikin nutsuwa tare da nuna ƙwarewar aiki.

Daga nan sai ya roƙi al’umma da su bawa Jami’an Hukumar haɗin kai da bin dokokin da aka shinfida kafin, yayin, da kuma bayan Kammala taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *