• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Barka Da Sallah: Zamu Tabbata Gwamnatin Kano Tayi Nasara a Ayyukan Cigaban Alumma — Shafi’u Hussaini

ByGlobal Tracker

Jun 30, 2023

DAGA: YAHAYA SADISU ALKASIM, KANO

 

Dan takarar shugabancin majalisar karamar Hukumar Ungogo Shafi’u Hussaini Kura ya taya jagoran jam’iyar NNPP na Kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf Murnar barka da Sallah.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Shafi’u Kura ya kuma taya Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da Jagororin jam’iyar NNPP a Karamar Hukumar Ungogo karkashin jagororin Bilya Musa da ma sauran al’ummar yankin da suka kasance a gaba-gaba wajen ganin jam’iyar NNPP ta yi Nasara a zaben da ya gabata ta ya su barka da Sallah.

Kura wanda kuma yake takarar shugabancin majalisar karamar Hukumar Ungogo ya ce matukar yayi Nasara akwai tsare-tsare daban-daban da yayi na gudanar da ayyukan Cigaban al’ummar yankin.

KU KARANTA: Mulkin Abba K. Yusuf na Sa’o’i 24 Ya Nuna Kishin Sa Da Cigaban Kano — Shafi’u Kura

Ya ce zai mayar da hankali wajen Cigaban fannin Ilimi da Inganta Lafiya, da samar da ayyukan yi da bada gudun mowa a Inganta tsaro da yaki da kwacen wayar hanu da sauran matsalolin da suke damun alumma a yankin.

Shafi’u Hussaini ya bukaci hadin Kai da goyon bayan al’ummar yankin domin samun nasarar ayyukan raya kasa.

Ya kuma jaddada kudirin Gwamnatin jihar Kano na dawo da jihar akan saiti ta hanyar rushe gine-ginen da akayi ba bisa ka’ida ba da karbe kadarorin gwamnati da tsohuwar Gwamnatin da ta shude ta mallakawa wasu tsirarun mutane.

Daga bisani ya bukaci al’ummar jihar Kano da su Cigaban da tallafawa Gwamnatin injiniya Abba Kabir Yusuf da goyon baya da yi mata addu’o’in samun nasara domin gwamnati ce wacce alumma suka zabe ta kuma dukkan matakai da tsare-tsaren da take gudanarwa ta na yin su ne domin Cigaban al’ummar da su ka zabe ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *