• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Muna Taya Kwankwaso, Abba, Gwarzo Murnar Barka da Sallah — Junaidu Dan-oga

ByGlobal Tracker

Jul 4, 2023

DAGA: YAHAYA SADISU ALKASIM, KANO

 

Dan takarar shugabancin majalisar karamar Hukumar Ungogo karkashin jam’iyar NNPP Mai alamar kayan marmari Alhaji Janaidu Rabi’u Dan-oga ya taya jagoran jam’iyar NNPP na Kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano injiniya Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo Murnar Barka da Sallah.

A tattaunawarsa da wakilin GLOBAL TRACKER, Dan-oga ya kuma taya Jagorori da shugabancin jam’iyar NNPP Murnar Barka da Sallah, tare da sauran al’ummar jihar Kano baki daya.

Janaidu Dan-oga bayyana cewa matukar ya sami damar zama Shugaban karamar Hukumar sa ta Ungogo zai tabbatar ya aiwatar da ayyukan Cigaban al’umma.

KU KARANTA: Barka Da Sallah: Zamu Tabbata Gwamnatin Kano Tayi Nasara a Ayyukan Cigaban Alumma — Shafi’u Hussaini

Ya bukaci hadin Kai da goyon bayan mutanen Ungogo domin samun nasarar da aka Sanya a gaba, ya na mai cewa akwai bukatar samar da ayyukan more rayuwa ga mutanen Ungogo sakamakon yadda yankin ya kasance koma baya idan an hada shi da sauran kananan hukumomin kwaryar birnin Kano.

Janaidu Dan-oga ya bukaci al’ummar Kano da su Cigaba da goyon bayan gwamnatin injiniya Abba Kabir Yusuf la’akari da manufofin da ta bijiro da su na cigaban mutanen Kano da ma Ungogo ba ki daya.

Dan takarar ya ce a gwamnatin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da ta shude ta gudanar da ayyukan Cigaban al’umma kuma matukar yayi Nasara salon mulkin kwankwasiyya na tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 zaiyi wanda suka hada da bada tallafin karatu da Inganta Lafiya da samar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin yankin da samar da ayyukan yi da gudanar da ayyukan raya kasa.

Yayi fatan zai samu hadin kan shugabancin jam’iyar NNPP na yankin da ma alumma domin aiwatar da kudirorin da ya Sanya a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *