• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zamu Ramawa Kwankwaso Abubuwan Alkhairin Da Yake Wa Mutanen Ungogo — Shafi’u Kura

ByGlobal Tracker

Jul 18, 2023

Dan takarar shugabancin karamar Hukumar Ungogo Shafi’u Ussaini Kura ya ce al’ummar karamar Hukumar Ungogo suna alfahari da irin Cigaban da jagoran jam’iyar NNPP na Kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yake kaiwa yankin da ma al’ummar su.

Ussaini Kura ya bayyana hakan ne lokacin da Kwankwaso ya halarci taron daurin Auren iyalan daya daga cikin jagororin jam’iyar NNPP a Ungogo.

Ya ce dukkan ayyukan da za’ayi a jihar Kano na cigaban Alumma sai Kwankwaso ya sa mutanen Ungogo a ciki saboda kishin sa na cigaban al’ummar yankin dama daya daga cikin jagororin jam’iyar NNPP na yankin Alhaji Hussaini Kura.

KU KARANTA: Muna Taya Kwankwaso, Abba, Gwarzo Murnar Barka da Sallah — Junaidu Dan-oga

KU KARANTA: Muna Kiran Gwamnan Kano Ya Kwato Tashar Malam Kato Da Tsohuwar Gwamnati ta Siyar — Balarabe Ahmed

Shafi’u Ussaini ya kuma taya jagoran jam’iyar ta NNPP na Kasa Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ban gajiya bisa halartar Daurin Auren da yayi a karshen Makon da ya gabata.

Kura ya kuma yabawa Dan majalisar Tarayya Mai wakiltar Ungogo da Munjibir Sani Wakili da Dan majalisar jihar Mai wakiltar Ungogo Aminu Sa’adu da Shugaban jam’iyar NNPP na Ungogo Alhaji Biliya Musa da sauran al’ummar yankin.

Ya kuma jaddada kudirin sa na neman takarar shugabancin karamar Hukumar ta Ungogo wanda acewarsa matukar sukayi nasara akwai tsare-tsare daban-daban da suka tanada domin Cigaban al’ummar yankin da ma jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *