• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Lawan Kolo Ya Bada Gudun Mowar Hada Kan Malamai Don Zabon APC a Zaben 2023 — Dr. Suleiman

ByGlobal Tracker

Jul 20, 2023

DAGA: KAMAL UMAR 

 

An bayyana Alhaji Lawal Kolo Geidam a matsayin cikakken Dan kishin kasa Wanda Kuma ya sadaukar da lafiyarsa da lokacin sa wajen wajen zagaye dukkanin jihohin dake arewacin najeriya domin hado kan Malaman makarantun gaba da sakandire da masana a jihohin domin marawa takarar Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shattima lokacin yakin neman zabe har aka Kai ga nasara.

Shugaban kungiyar gamayyar Malamai da Masanan ta kasa Dakta Suleiman Isyaku Muhammad ne ya bayyana hakan a wajen taron da kungiyar ta shiryawa kungiyoyi irin ta a birnin tarayya Abuja domin shirya yadda za’a bada lambar yabo ga Alhaji Lawal Kolo Geidam bisa irin gudunmawar daya bada har Shugaba Tinubu da Kashim Shattima suka Kai ga nasara.

Dakta Suleiman ya ce samun mutane irinsu Alhaji Lawal Kolo Geidam a tsakanin al’umma abu ne Mai matukar tasiri duba da yadda yake sadaukar da Kansa da komai nasa domin ganin al’ummar arewacin kasar nan sun samu kyakkyawar makoma da ingantacciyar rayuwa daga gwamnatin tarayya.

Alhaji Lawan Kolo Geidam da Matemakin Shugaban kasa Kashim Shettima.

Wasu daga cikin ‘yan kungiyoyi daban daban da suka halarci taron bada lambar yabon ga Alhaji Lawal Kolo Geidam sun bayyanawa jami’in yada labaran kungiyar ta Malamai da Masanan dake makarantun gaba da sakandiren kasar nan Kamal Umar Kurna cewa bawa kolo lambar yabon na a matsayin Wani salo na nuna gamsuwa da rawar da ya taka a baya yake Kuma cigaba da takawa har a yanzu domin inganta rayuwar al’ummar jihohi 19 dake arewacin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *