• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Nan Da Mako Guda Zamu Kammala Kwashe Dukkan Sharar Da Aka Sake Tarawa — Dan Zago

ByGlobal Tracker

Jul 25, 2023

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassada Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya ce nan da mako guda al’ummar jihar nan zasu shaida yadda hukumar sa zata kwashe dukkanin wata shara aka jibge akan titunan jihar nan domin gujewa ambaliyar ruwa.

Dan zago ya bayyana hakan lokacin da tawagar ‘yan jaridun dake aiki a gidan gwamnatin jihar Kano suka Kai masa ziyarar aiki a ofishinsa.

KU KARANTA: Za Mu Yaki Zubar Da Shara Ba Bisa Ka’ida Ba Cikin Dare — Dan Zago

Ya ce duba da irin ayyukan da hukumar sa ta gudanar tun bayan daya karbi ragamar ta, al’ummar jihar Kano nada kyakkyawan zato da Sanya rai akan aikace aikacen a yanzu wanda hukumar tasa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen share musu hawayensu.

Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban ‘yan jaridun dake gudanar da ayyukansu a gwamnatin kano Adamu Dabo Dawakin Tofa ya ce sun kai ziyarar ne a wani mataki na ba zata domin ganewa idanunsu irin aikace aikacen hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *