Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Salman Dogo da Sanatan Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila sun ziyarci gurin da akayi rikici tsakanin al’umma da jami’in yan sanda a Kauyen Jigaware kusa da Darki a karamar hukumar Wudil.
Idan za’a iya tunawa a jiya jaridar GLOBAL TRACKER ta kawo muku rahoton yadda aka sami rikici tsakanin jami’an yan sanda da wani direban lamarin da ya fusata al’umma suka farwa Yan sanda da duka inda wani daga cikin jami’an yayi harbi don tsara da rayuwarsa.

Ana zargin Lamarin dai yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku ciki harda wani saurayi da bai cika mako guda da yin Aure ba, zargin da wannan jaridar ba ta Kai ga tantancewa ba.
Amma, a bayanan da GLOBAL TRACKER ta tattaro, kwamishinan Yan Sandan jihar Kano da Kawu Sumaila sun ziyarci gidan marigayin inda suka yi wa yan uwa ta’aziyar rashin da suka yi.

Kawu Sumaila ya bukaci al’ummar yankin na Jigawa da Darki da su kwantar da hankalinsu inda ya bukaci kwamishinan Yan sanda ya bada umarnin gudanar da sahihin bincike don gano musabbabin faruwar al’amarin don gudun sake afkuwar hakan a nan gaba.