• Mon. Nov 16th, 2026

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gwamnan Kano Ya Saki Matarsa Da Ta Kai Shi Kara Kotu

BySani Magaji Garko

Nov 16, 2026

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da sakin Matarsa Zainab Musa Kwankwaso wacce ta kasance ’ya ga tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron biyan kuɗin ƴan fansho a fadar gwamnatin Kano ranar Litinin, inda ya ce ya amince da zama mai mace ɗaya a yanzu, amma yana da niyyar sake aure nan gaba.

Ya kuma ce ya umurci Kwamishinan yaɗa labarai da ya sanya sanarwa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta domin gayyatar matan da ke sha’awar auren gwamnan.

KU KARANTA: Rikicin Aure: Gwamnan Kano Ya Hada Tawaga Mai Karfi Don Tattaunawa Da Kwankwaso

Yusuf ya bayyana cewa ya ji daɗin matakin da ya ɗauka, tare da roƙon Allah Ya azurta shi da mutanen kirki a rayuwarsa.

Hakan na zuwa ne bayan Zainab Musa Kwankwaso ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gudu, Abuja, ranar Asabar din da ta Gabata.

Takardar sammaci mai lamba CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

Abba Yusuf da Zainab sun yi aure ne a ranar 29 ga Yulin 2006, lokacin da gwamnan ke aiki a matsayin hadimi ga mahaifinta, Sanata Rabiu Kwankwaso, kuma sun haifi ’ya’ya shida da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *