Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kafa tawaga mai karfi da ta kunshi shugabannin siyasa, malamai, dattawa, da kuma masu ruwa da tsaki a jihar Kano, domin ziyartar gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke Abuja.
Wannan mataki wani sabon yunkuri ne na sasanta rikicin aure da ke faruwa tsakanin Gwamnan da matarsa, Hajiya Zainab Musa Kwankwaso, wacce ita ce ‘yar tsohon Gwamnan Jihar Kano.
Wata majiya mai tushe daga Gidan Gwamnatin Kano, wacce ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, shi ne zai jagoranci tawagar.
KU KARANTA: ‘Yar Kwankwaso Kuma Matar Gwamnan Kano Ta Kai Ƙara Don Neman Saki, Ta Amince Da Mayar Da Sadaki
Sauran fitattun mutanen da ake sa ran za su kasance cikin tawagar sulhun sun hada da Khalifa Sheikh Qaribullah Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, shugaban darikar Qadiriyya a Najeriya da Yammacin Afirka da Sheikh Abdulwahhab Abdallah, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma mamba a Majalisar Shura ta Jihar Kano; da Malam Tijjani Yammota, tare da wasu dattawa da shugabannin siyasa da ake girmamawa.
A cewar majiyar, ana sa ran tawagar za ta tashi daga Kano zuwa Abuja domin rokon Sanata Kwankwaso ya sake duba matsayinsa, tare da ba da damar ‘yarsa, Hajiya Zainab Musa Kwankwaso, ta koma Gidan Gwamnati.
Haka kuma, ana sa ran tawagar za ta yi kira ga bangarorin biyu da su warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, fahimtar juna, da kuma girmama auren, maimakon barin bambance-bambancen siyasa su kara dagula lamarin.
Majiyar ta kara da cewa, Gwamna Yusuf har yanzu yana kaunar matarsa kuma yana da kudurorin ganin ya kare aurensu, musamman saboda ‘ya’yansu guda shida.
An ruwaito cewa ma’auratan sun shafe sama da shekaru 20 tare, inda suka daura aure a ranar 29 ga watan Yuli, 2006.
Majiyar ta bayyana lamarin a matsayin wani abu da ba a saba gani ba, idan aka yi la’akari da tsawon lokacin da suka shafe tare da kuma iyalin da suka gina, inda ta jaddada cewa ya kamata a ba da fifiko ga walwala da makomar ‘ya’yansu.
“Gwamna Yusuf har yanzu yana kaunar matarsa, wacce ita ce mahaifiyar yaransa, kuma har yanzu yana daukar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mahaifinsa. Wannan lamari ne na iyali da ke bukatar fahimtar juna, sulhu, da kuma shiga tsakani na manyan mutane masu mutunci,” in ji majiyar.
Majiyar ta kara da cewa, “Bai kamata a bari siyasa ta shiga tsakanin miji da mata da ke kaunar juna ba, musamman bayan sun shafe sama da shekaru 20 a tare a matsayin ma’aurata kuma suna da yara shida. Gwamna yana son zaman lafiya, kuma mun yi imani cewa tattaunawa da shiga tsakani na wadannan mutane masu mutunci na iya taimakawa wajen dawo da fahimtar juna tsakanin iyalai biyun,” in ji majiyar.
Lokacin da aka tuntubi Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, domin tabbatar da wannan bayani, ya bayyana cewa bai da masaniyar kafa wata tawaga ta musamman.
Ya kara da bayanin cewa lamarin Abu ne tsakanin maaurata, kuma ba ya bukatar bayani a bainar jama’a.
Kwamishinan ya ce, “bisa ka’idojin aikinmu, batutuwan da suka shafi rayuwar Gwamna ta sirri ba za a iya tattauna su ba sai an samu izini daga gunsa; saboda haka, ina kira ga dukkan jami’an gwamnati da su nuna takatsantsan dangane da wannan batu.”
Majiya: Checks Naija.