Honarabil Suleiman Abdurrahaman Kawu Sumaila ya yi nasarar zama Sanatan Kano ta Kudu a majalisar Dattawa ta kasa.
Babban baturen zaben yankin Farfesa Ibrahim Barde ne ya bayyana samakon zaben a cibiyar tattara Sakomakon da ke Karamar hukumar Rano.
Ya ce Kawu Sumaila na jam’iyar NNPP ya samu kuri’u 319,857 inda abokin hamayyarsa Kuma sanata Mai barin gado Kabiru Gaya ya Sami kur’u 192,518.
“Saboda haka bayan cika dukkan kaidojo, Kawu Sumaila ya zama sanatan Kano ta Kudu”, inji Farfesa Ibrahim Barde.
Akwai Karin bayani….