• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

DA DUMI-DUMI: Sanata Kawu Sumaila Ya Fice Daga NNPP zuwa APC

BySani Magaji Garko

Apr 23, 2025

Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya fice daga jam’iyar NNPP mai mulkin Jihar Kano zuwa APC mai mulkin tarayyar Nigeriya.

Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook wanda mai magana da yawunsa Abbas Hotoro ya tabbatarwa GLOBAL TRACKER.

Idan za’a tunawa ko a makon da ya gabata GLOBAL TRACKER ta rawaito muku cewa Kawu Sumaila da wasu manyan Yan siyasa masu rike da mukamai daban-daban a NNPP sun ziyarci shugaban jam’iyar APC a Abuja.

KU KARANTA: Shugaban APC, Ganduje Ya Yi Ganawar Sirri Da Kawu Sumaila, Ali Madaki Da Sauran Yan NNPP

Fitar kawun na zuwa bayan da aka rika samun tankiya tsakanin Sanatan da masu mara masa baya Yan majalisar wakilai uku wato Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Alhassa Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini da kuma shugabancin jam’iyar NNPP tsagin Hashimu Suleiman Dungurawa.

Akwai Karin bayani….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *