A kalla mutane 11 ne suka rasu yayin da wasu 9 suka samu raunuka daban-daban sakamakon Hatsarin Mota a Kauyen Beguwa kan titin Sankara cikin karamar hukumar Ringim a Jihar Jigawa.
Rahotanni sun bayyana cewa Hatsari yana da nasaba da daukar mutane da suka wuce kima da kuma zargin ganganci da ake yiwa direban motar wanda yana cikin mutanen 9 da suka sami raunuka.
SP Lawan Shiisu Adam, kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce da zarar direban ya murmure zasu dauke shi daga asibitin da ake kula da lafiyarsa zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘Yan Sandan Jihar domin cigaba da gudanar da bincike.
“Da zarar driver ya murmure, zamu tasa keyar sa zuwa SCID don tuhumar sa da kashe mutane da gangan,” inji Shiisu.
Akwai karin bayani….