A dai-dai lokacin da gangamin yakin neman zaben shekar 2027 ke kankama, babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Gombe ta umarci Jam’iyyar PDP da ta sake gudanar da zaben fidda gwani domin tantance dan takararta na gwamnan Jihar Gombe.
Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin bayan sauraron karar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana kalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin dan takarar jam’iyyar ta PDP.
KU KARANTA: PDP Ta Tsayar Da Isa Ali Pantami Takarar Gwamna a Gombe
Garry ya kalubalanci tsayar da Pantami bayan PDP ta sanar da shi a matsayin dan takara tilo a ranar 26 ga Yuni 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani da ya dace ba.
Pantami ya koma PDP ne bayan da Jam’iyar APC mai mulkin Jihar ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na yarjejeniya.
Sai dai kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaben fidda gwani bisa ka’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zabe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
A baya, Pantami ya samu tikitin PDP ne ta hanyar amincewa da baki yayin zaben fidda gwani na Jam’iyar.
Shigar Pantami PDP ya ci karo da kalubale kala-kala sakamakon yadda Sheik Pantami yayi da sukar Jam’iyar a karatuttukar da yayi a shekarun baya.