• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rasha ta Kama Dan Jaridar Amurka Bisa Zargin Leken Asiri

ByGlobal Tracker

Mar 30, 2023

Hukumar tsaron cikin gidan ta kasa Rasha ta ce ta kama wani dan jarida Ba’Amurke da ke aiki da mujallar Wall Street Journal a Rasha kan zargin yi mata leken asiri a madadin Amurka a kasarta.

Sanarwar wata alama ce ta kokarin da gwamnatin Rasha ke yi na dakile masu caccakarta, lamarin da ta zafafa aiwatarwa tun bayan da ta fara yaki da kasar Ukraine a shekarar 2022 da ta gabata.

Hukumar tsaron ta Rasha ta dakile wasu ayyukan da dan jaridan kasar Amurkan, Evan Gershkovich, ke yi ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa ma’aikacin na mujallar Wall Street Journal yana yi wa gwamnatin Amurka ne aiki.

Mujallar Wall Street Journal ta damu matuka a game da lafiyar Gershkovich.

KU KARANTA: AU Ta Gamsu Da Shirin Nigeria Na Gudanar Da Sahihin Zabe — Kenyyata

Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta “Reporters Without Borders (RSF)” ta ce ta kadu a game da kama dan jaridar, wanda ta ce ya yi kamanceceniya da ramuwar gayya.

Kungiyar RSF ta ce Gershkovich yana bincike ne a kan kamfanin tsaro mai zaman kansa, Wagner, wanda ke taka mahimmiyar rawa a yakin da Rasha ke yi da kasar Ukraine.

Hukumar tsaron cikin gida Rashar ta tabbatar da cewa Gershkovich, mai shekaru 31 wanda ke aiki da tantancewar ma’aikatar harkokin wajen Rasha ya shiga hannunta ne saboda zargin yana tattara bayanai a kan ayyukan sojin Rasha.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Maria Zakharova ta ce an kama Gershkovich dumu-dumu cikin aikata abin da ake zarginsa da shi.

KU KARANTA: Yan Sanda a Amurka Na Shirin Kama Donald Trump

Kafin komawa Wall Street Journal, Gershkovich ya yi aiki da kamfanin dillancin labaran Faransa wato AFP.

Yana jin harsunan Ingilishi da Rashanci sosai, kuma ya taba aiki da a matsayin wakilin shafin labarai na Moscow Times, wanda ke wallafa labarai da harshen Ingilishi.

Iyayensa sun koma Amurka tun yana yaro.

 

RFI Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *