• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Masarautar Kano Zata Tallafawa Matuka Akori-kura Don Samun Matsuguni na Din-din-din

ByGlobal Tracker

Apr 13, 2023

DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO

 

Masarautar Kano ta sha alwashin tallafawa kungiyar matuka motocin Akori-kura ta (NURTW) reshen railway dake Kano cikakkiyar gudunmawar da ta kamata domin ciyar da harkokin sufuri gaba.

Hakimin karamar hukumar Fagge Alhaji Muhamud Ado Bayero Turakin Kano ne ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara domin taya shi murna tare da bashi lambar girmamawa, bisa Karin girma da ya samu.

Muhamud Ado Bayero ya ce fadarsa a shirye take wajen tallafawa kungiyar matuka motocin Akori-kura ta railway, wajen inganta sana’arsu yadda ta kamata, duba da irin jajircewar da yan kungiyar suke da shi a fannin samarwa matasa ayyukan dogaro da kawunansu.

Ya kuma hori yan kungiyar da su kasance masu bin dokokin tuki da kaucewa gudun ganganci a yayin gudanar da ayyukansu musamman, idon suka hau manyan tituna.

Ya ce kofarsu a bude take ga duk wata bukata da kungiyar take nema domin ciyar da harkokin sufuri da kare martabar masarautar Kano da tallafawa matasan a fannoni da dama.

KU KARANTA: Matuka Akori-kura Sun Roki Gwamnati Matsuguni Na Din-din-din

A jawabinsa, shugaban kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen railway dake nan Kano, Abubakar Dan-iya Bala ya ce sun kawo zayarar ne domin taya Hakimi murna bisa Karin girman daya samu daga Tafidan Kano zuwa Turakin Kano wanda masarautar Kano ta nada shi.

Dan-iya Bala ya kuma ce kungiyar tana bukatar fadar Hakimin Fagge da ta shige musu gaba domin samar musu gurin tsayawa na din-din-din karkashin Gwamnati.

Shugaban ya ce, duba da gudunmawar da fadar Hakimin take baiwa Yan kungiyar ya Kara musu kaimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *